(ABNA24.com) Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da bayani a jiya Laraba da dare da a ciki ta yi kira ga gwamnati da ‘yan sandan kasar Faransa da su daina amfani da karfi akan masu Zanga-zanga.
Ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta wallafa sanarwar ce a shafin Twitter, inda ta ce; bai kamata gwamnati da ‘yan sandan kasar ta Faransa su rika amfani da karfi akan mutanen da ba su dauke da wani makami ba.
Bugu da kari ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta kirayi gwamnatin Faransan da ta biya wa masu Zanga-zangar bukatunsu maimakon amfani da karfi akansu.
/129
30 Janairu 2020 - 05:48
Lambar labari: 1006375
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da bayani a jiya Laraba da dare da a ciki ta yi kira ga gwamnati da ‘yan sandan kasar Faransa da su daina amfani da karfi akan masu Zanga-zanga.